Bayan wata mummunar gobara da ta tashi a tashar Shahid Rajaee da ke Bandar Abbas, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a cikin wani sako da ya aike da shi, yayin da yake jajantawa iyalan mamatan, ya umarci jami'an tsaro da na shari'a da su yi cikakken bincike tare da bankado duk wani sakaci ko ganganci a cikin wannan lamari tare da bin ka'ida.
Nassin sakon Jagoran juyin juya halin Musulunci shi ne kamar haka;
بسم الله الرّحمن الرّحیم
انا لله و انا الیه راجعون
Da Sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai.
Daga Allah Mu Ke Kuma Gare She Mu Ke Komawa
Mummunan gobarar da ta afku a tashar jirgin ruwa ta Shahid Rajaee ta haifar da bakin ciki da damuwa.
Ana buƙatar jami'an tsaro da na shari'a da su yi cikakken bincike, gano duk wani sakaci ko ganganci, tare da bin sa bisa ka'ida.
Dole ne dukkan jami'ai su dauki kansu da alhakin hana afkuwar bala'i da ke dauke da asara. Ina rokon Allah ya jikan wadanda suka rasu da gafara, ya kuma baiwa iyalansu hakurin jure rashin, ya kuma bada lafiya ga wadanda suka samu raunuka a wannan mummunan lamari. Ina mika godiya ga jama'a masu karamci wadanda suka shirya bayar da gudummawar jini ga wadanda suka jikkata a lokacin bukata.
والسلام علیکم و رحمةالله
Sayyid Ali Khamenei
27 Afrilu,2025
Your Comment